Najeriya Na Bukatar Naira Tiriliyan 21 Don magance matsalar karancin gidaje – Shettima

0
20

NIJERIYA na bukatar Naira Tiriliyan 21 domin magance gibin gidaje a kasar, a cewar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.

Ya bayyana haka ne a yayin da ake kaddamar da ginin katafaren gidaje guda dari biyar da gwamnatin jihar Sokoto za ta gina.

A wata sanarwa da Olusola Abiola, Daraktan ofishin mataimakin shugaban kasa, Sanata Shettima ya bayyana cewa Najeriya na da gibin gidaje na gidaje miliyan ashirin da takwas.

Sai dai ya yabawa gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto bisa kokarin da yake yi na magance bukatun gidaje na jama’ar sa.

Aikin da aka gudanar a karamar hukumar Wamakko zai lakume wa gwamnatin jihar zunzurutun kudi har naira biliyan 7.3.

Gwamna Aliyu ya ce gidan na ma’aikatan gwamnati ne kuma za a sayar musu da su idan an kammala su bisa ga magidanta.

Firdausi Musa Dantsoho