GWAMNA LAWAL YA KADDAMAR DA RABON KAYAN ANFANIN GONA A KANANAN HUKUMOMIN BAKURA, MAFARA DA MARADUN

0
9

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana muhimmancin noma ga tattalin arzikin jihar Zamfara, inda ya ce galibin karfin tattalin arzikin jihar noma ne.

A yau litinin, Gwamna Lawal ya kaddamar da rabon kayayyakin noma a kananan hukumomi uku (3) – Bakura, Mafara da Maradun a ci gaba da bikin kaddamar da shirin farfado da tattalin arziki na COVID-19 a karkashin FADAMA III.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce Gwamna Lawal ya bukaci manoman jihar da su yi amfani da damar da suka samu wajen kara yawan amfanin gonakin da suke nomawa tare da bayar da gudunmuwarsu ga ci gaban jihar.

Ya kara da cewa kayayyakin amfanin gona da aka raba sun hada da takin zamani, ingantattun tsirrai, da sauran kayayyakin amfanin gona.

A yayin kaddamar da shirin a karamar hukumar Bakura, Gwamna Lawal ya tabbatar wa manoman kudurin gwamnatin jihar na tallafa wa fannin noma domin tabbatar da ci gabansa.

“Baya ga raba kayan amfanin gona, gwamnatina za ta aiwatar da ayyuka da dama a karamar hukumar Bakura. Wadannan ayyuka sun hada da karin gine-gine a kwalejin noma da kimiyar dabbobi ta Bakura, gyaran babbar asibitin garin Bakura, gyara makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati, gyara makarantar sakandiren gwamnati dake Yarkofoji, gyaran gonakin noman Bakura. , Gina Kotun Majistare, Bakura, Gina masarauta da sauran ayyuka da dama Insha Allahu.

A taron kaddamar da shirin a karamar hukumar Mafara, Gwamna Lawal ya ce shirin zai inganta noma sosai a karamar hukumar Talata Mafara.

“Ina so in yi kira ga wadanda zasu ci gajiyar wannan tallafi da su yi amfani da shi yadda ya kamata. Muna da sauran ayyuka ga al’ummar karamar hukumar Talata Mafara.

“Gwamnatina za ta aiwatar da ayyuka a jami’ar jihar Zamfara, Talata Mafara, kwalejin kere-kere ta, Abdu Gusau, gina cibiyar bada Agajin Gaggawa, Tafkin Kifi don noman kifi, gyare-gyare tare da ƙarin gine-gine a babbar asibitin Talatar Mafara, gina ofishin Ilimi na yankin Zamfara ta yamma, Samar da Gidajen zama na alkalan kotun daukaka kara, Sashen Talata Mafara, Gina Cibiyar Matasa ta yankin, Gina cigaban Ilimin Mata, Talata Mafara, Gyaran Makarantar Sakandaren Gwamnati, Agwaragi, Talata Mafara, gyarawa da fadada aikin likitancin dabbobi, inganta masana’antar ruwa na Talata Mafara, da sauran ayyuka da dama Insha Allah.”

A karamar hukumar Maradun Gwamnan jihar Zamfara ya jaddada cewa tattalin arzikin jihar ya dogara ne akan noma. Sakamakon haka, shirin na COVID-19 ya maida hankali ne kawai kan tallafawa fannin noma.

“Ina fatan wannan yunkuri zai taimaka matuka wajen inganta ayyukan noma a karamar hukumar Maradun da ma jihar Zamfara baki daya.

“Karamar hukumar Maradun, kamar sauran sassan jihar, za ta ci gajiyar ayyuka da dama a cikin kasafin kudin 2024. Wadannan ayyuka sun hada da gyaran makarantar Sakandaren Gwamnati dake Gora, inganta babbar asibitin Maradun, gina titin Maradun-Makera da Maradun-Magami-Faru, da gina ofisoshi na ’yan sandan tafi da gidanka, kotun majistare, da gina gidajen zama ga alkalai. Haka kuma akwai sauran ayyukan da aka tsara insha Allahu”.

SULAIMAN BALA IDRIS

Babban mataimaki na musamman (kafafen sadarwa da watsa labarai) ga Gwamnan Zamfara

Fabrairu 05, 2024