Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta bude tattaunawa da gwamnatin jihar Nasarawa da nufin hada kai wajen samar da layin dogo da hanyoyin mota daga Apo zuwa Keffi, da kuma kammala aikin hanyar da ta tashi daga Barikin Abacha zuwa Masaka.
Ministan babban birnin tarayya, Nyesome Wike ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Juma’a a lokacin da gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja.
Wike ya ba da tabbacin cewa “ba za a iya karasa rawar da jihar Nasarawa ta taka ba dangane da ci gaban babban birnin tarayya Abuja. A sirri, mun yi magana game da wannan, kuma ga duk wanda ya fahimci cewa FCT na nan a cibiyar; muna da iyaka da jihohin Neja, Kogi, Kaduna da Nasarawa. Amma duk jihohin Nasarawa ita ce babba, kuma tana kusa da mu. Don haka, idan muna son yin magana game da ci gaba, dole ne mu yi aiki tare, wanda ke da mahimmanci.
Ministan ya gano cewa batutuwa da yawa da aka tattauna da magabata. Matsalar da ake da ita ita ce yawan bayar da kwangila ba tare da an karasa ba. Muna da aiyuka da dama , don haka muna kokarin ganin yadda za mu iya gano manyan abubuwan da muke bukata wadanda za su bunkasa ci gaba.
“Ba za mu iya magance dukkan matsalolin ba amma mu yi dai dai gwargwadon iyawar mu mutane za su yaba da cewa kun aza harsashin bude wuraren biyu. Zan iya tabbatar muku cewa za a yi aiki tare. Batun tsaro ma yana da muhimmanci. Muna nan a karshe, duk abin da ya faru a jihohin Neja, Nasarawa, Kogi da Kaduna, su (mutane) suna gudowa nan (Abuja). Don haka lamari ne da ya kamata mu hada kai don magance matsalar rashin tsaro, ba za mu iya guduwa daga gare shi ba.
“Ina kokarin ganin yadda za mu yi taro tsakanin jihohi makwabta da FCT, domin mu hada kawunanmu mu samar da tsarin da za mu ga yadda za mu magance matsalar rashin tsaro, domin ba za mu iya yin shi kadai ba. Don haka mutane irin ku ina ganin za su tabbatar da cewa za a iya cimma sabon tsarin fatan shugaban kasa. Ka tabbatar da cewa tare za mu yi aiki domin tabbatar da cewa matsalar tsaro da ci gaban al’umma ya zama tarihi.
Daga Fatima Abubakar.