Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamnan Gombe Ya Kaɗa Ƙuri’a A Mazaɓarsa Dake Jekadafari   

0
24

Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamnan Gombe Ya Kaɗa Ƙuri’a A Mazaɓarsa Dake Jekadafari

 

Daga Yunusa Isa, Gombe

 

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya bi sahun sauran masu kaɗa kuri’a yau Asabar don kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi dana kansiloli da aka gudanar a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar.

 

Gwamna Inuwa Yahaya ya kaɗa ƙuri’ar tasa ce a mazabarsa ta Yahaya Umaru mai lamba 010 dake unguwar Jekadafari a Ƙaramar Hukumar Gombe da misalin ƙarfe 11:15 na safe, tare da ɗaruruwan masu kaɗa ƙuri’a da suka yi dandazo don kaɗa ƙuri’a a zaɓen.

 

Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kaɗa kuri’ar, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana jin daɗinsa da yadda zaɓen ya cika duk ka’idojin da suka wajaba, tare da tabbatar da daidaito ga dukkan jam’iyyun siyasa don su shiga cikin zaɓen.

 

Gwamnan yace zaɓen ya baiwa al’ummar jihar damar zaɓar shugabannin ƙananan hukumomi da na gundumomi bisa tsarin demokraɗiyya da doka.

 

“Kuna ganin yadda jama’a suka yi jerin gwano tun sassafe don yin amfani da ‘yancinsu na kaɗa kuri’a, nima na bi sahunsu wajen kaɗa ƙuri’a, ina farin cikin ganin yadda ake gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana a nan da kuma faɗin Jihar Gombe baki ɗaya bisa ga rahotannin da na samu.

 

Yana da matuƙar muhimmanci a tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe don ɗorewar demokraɗiyyarmu, shi ya sa muka bada dama ga dukkan jam’iyyun siyasa, hatta jam’iyyun adawa sun shiga wannan zaɓe.

 

Gwamnan ya ƙara da cewa “Wannan zaɓe yana da matuƙar muhimmanci domin ya baiwa ‘yan ƙasa damar zaɓar shugabanninsu a matakin ƙananan hukumomi da kuma gundumomi, duba da irin nasarorin da gwamnatinmu ta samu, ina da yaƙinin cewa jama’a za su marawa jam’iyyarmu baya, farin cikin dake bayyane a fuskokinsu ya nuna cewa suna murna da wannan lamari, na jam’iyyar APC, kuma ina da ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyarmu za ta samu nasara a dukkan kujerun da aka fafata a wannan zaɓe,”

 

Gwamnan ya kuma yabawa hukumar zaɓe ta jihar (GOSIEC) da jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu na ganin an gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin ba tare da wata matsala ba, inda ya yabawa hukumar zaɓen bisa bin kyawawan tsare-tsare, wanda ya taimaka wajen gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci.

 

Da yake mayar da martani dangane da iƙirarin da wassu fusatattun jam’iyyu suka yi, na ƙoƙarin ƙalubalantar sakamakon zaɓen, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa tuni aka kafa wata kotun sauraron kararrakin zaɓe ta ƙananan hukumomi da za ta saurari duk wani koke ko korafe-korafe da ka iya tasowa daga zaɓen.

 

Ya kuma buƙaci al’ummar jihar su kwantar da hankula tare da nuna kyawawan ɗabi’u yayin da suke jiran sakamakon zaɓen.

 

 

Hafsat Ibrahim