Daga Yunusa Isah kumo
Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Da Gwamna Inuwa Da Sauran Shugabannin Arewa Maso Gabas Sun Ƙaddamar Da Shirin ASSEP Don Haɓaka Ilimi da Sana’o’i
A jiya Asabar ce Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da sauran shugabannin Arewa Maso Gabas suka ƙaddamar da Shirin Inganta Ilimin Sakandare (ASSEP) a Bauchi.
Wannan shiri, wanda hukumar raya yankin Arewa maso Gabas (NEDC) ke aiwatarwa, yana da nufin inganta ilimi da koyar da sana’o’i ga ɗaliban da suka kammala karatun sakandare a faɗin jihohin Arewa Maso Gabas guda shida.
A yayin ƙaddamarwar, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jaddada muhimmiyar rawar da ilimin sakandare ke takawa tamkar wani tsani bayan karatun firamare, yana mai jaddada ƙalubalen tarihin yankin na Arewa maso Gabas wajen aiwatar da tsare-tsaren ilimi bai ɗaya da kuma shawo kan ƙalubalen da al’adu ke yi ga ilimin boko.
Yace Yankin na Arewa Maso Gabas yana fama da ƙarancin shigan yara makarantun sakandare, wadda kwata-kwata bai wuce kaso 19 cikin ɗari yake da shi ba, idan aka kwatanta da alƙaluman shiga yara makarantun sakandare a ƙasa, wadda ya kai kaso 39 cikin ɗari.
Shettima ya yabawa gwamnonin shiyyar bisa haɗin kai da jajircewarsu wajen inganta yankin, inda ya yaba da ƙoƙarinsu na ganin an haɗa kai don cike giɓi a harkokin mulki.
Manajan Daraktan hukumar ta NEDC, Mohammed Goni Alkali ya yi ƙarin haske kan manufofin shirin na ASSEP, waɗanda suka haɗa da inganta makarantun gaba da sakandare, da bunƙasa sana’o’in hannu, da kuma inganta ƙwarewar malamai.
Alkali ya jaddada aniyar shirin na mayar da hankali kan shirye-shiryen Kimiyya da Fasaha da Injiniyanci, da Lissafi wato (STEM) da kuma sadarwa, waɗanda ke da muhimmanci wajen bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire, da tunani mai zurfi a tsakanin matasa.
Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe.
Hafsat Ibrahim