Daga Fiddausi Umar Aliyu
Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa da LEADERSHIP cewar an dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da majalisar dokokin jihar, ta yi wa dokar da ta ƙirƙiro sabbin masarautu huɗu a lokacin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kwaskwarima tare da rushe su a yau
A cewar majiyar “Bayan zartar da dokar Sanusi ya dawo kan kujerarsa babu bukatar sanarwa, kawai gwamna ake jira ya tabbatar.”
Tun da farko tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne, ya yi amfani da dokar wajen tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Sarkin Kano na 14 a 2020.
Tun da fari gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da zai sanya hannu idan majalisar ta amince da gyaran dokar.
Shugaban masu rinjaye kuma wakilin mazabar Dala, Hussein Dala ne, ya gabatar da kudirin gyara dokar a yayin zaman majalisar na ranar Talata.
Hafsat Ibrahim