Jami’an ‘yan sanda sun kama wani ma’aikacin kamfanin Point of Sale wanda rahotanni suka bayyana cewa ya yi zagon-kasa ne bayan da wani bankin kasuwanci ya tura N280m cikin kuskure a asusun sa.
Rundunar ‘yan sanda ta kama ma’aikacin POS mai suna Alfa Rafiu ranar Litinin a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
An tattaro cewa wanda ake zargin mazaunin unguwar Akuji ne, a unguwar Abayawo a karamar hukumar Ilorin ta yamma.
A cewar majiyoyin da ke yankin da ke da masaniya kan lamarin, Rafiu ya ci gaba da kashe makudan kudade bayan da ya samu sanarwar a cikin rukunoni makonnin baya.
“Amma maimakon ya jawo hankalin bankin da ya karkatar da makudan kudade a bisa kuskure, sai ya ci gaba da kashin kudi
“Rafiu ya sayi gidaje, da motoci kuma ya dauki nauyin mutane zuwa yin aikin Umrah a kasar Saudiyya. Ko da yake ya kasance mai kyauta ga mutane da yawa a cikin al’umma, wasu mazauna yankin sun yi mamakin dukiyarsa kwatsam a matsayinsa na ma’aikacin POS,” in ji daya daga cikin majiyoyin.
An tattaro cewa daga baya masu binciken bankin sun gano kuskuren inda suka tura jami’an tsaro bayan an kama Rafiu aka koma da shi Legas.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na ‘yan sanda daga Alagbon-Close, Ikoyi, Legas ne suka kama shi wanda hakan ya sa muka fita daga hurumin binciken,” in ji Okasanmi.
Daga Fatima Abubakar.