Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja, za ta gudanar da aikinta na farko na ilimi da wayar da kan Alhazai na bana a ranakun Asabar 18 da Lahadi 19 ga Maris, 2023.
A wata sanarwa da kakakin hukumar Muhammad Lawal Aliyu ya fitar ta bayyana cewa tuni aka hada malaman addinin musulunci domin gudanar da atisayen da aka shirya gudanarwa a sansanin Hajjin dindindin na FCT dake Basan Jiwa kusa da filin jirgin saman Nnamdi Azikwe dake Abuja.
Muhammad Lawal ya bayyana cewa, za a gudanar da atisayen ne a matakai domin baiwa mahajjata damar samun haske kan ayyukan hajji da kuma sabbin tsare-tsare na aikin hajjin bana da hukumomin Saudiyya da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON suka bullo da su.
Jami’in Hulda da Jama’a ya shawarci Alhazan yankin da su ka fito domin gudanar da aikin hajjin bana da su shiga dukkan shirye-shiryen da hukumar ta shirya da nufin taimaka musu wajen samun aikin hajji mai karbuwa.
Ya shawarci mahajjata musamman wadanda suka fara aikin Hajji, da su yi amfani da wannan atisayen da kuma inganta iliminsu na Musulunci kan ayyukan Hajji da shiryarwa mai kyau don samun darajar kudinsu.
Don haka ya gargadi dukkan maniyyatan da har yanzu ba su dawo da fom din su da suka kammala ba ko kuma su mika fasfo dinsu na kasa da kasa da su yi hakan don baiwa hukumar damar fara gudanar da takardun tafiyar.
Hakazalika, sanarwar ta yi kira ga maniyyatan da suka kasa zuwa aikin Hajjin bara da su sabunta takardunsu ga Hukumar yayin da aka bukaci wadanda suka ajiye kasa da mafi karancin Naira Miliyan 2.5 da su cika ajiya domin neman kujerar aikin Hajjin 2023.
Hukumar ta kuma bukaci wadanda suka yi ajiya a aikin hajjin da suka gabata amma suka kasa yin aikin saboda wani dalili na su kai rahoto ga hukumar da ainihin takardar biyansu domin bayyana sha’awarsu ta shiga aikin hajjin bana ko kuma a mayar musu da su.
Ya bayyana cewa matakin ya zama dole domin baiwa hukumar damar samar da ainihin jerin sunayen Alhazan da za su gudanar da aikin a bana.
Sanarwar ta bayyana cewa Alhazan da suka ajiye har zuwa mafi karancin albashi na Naira miliyan 2.5 zuwa sama ne kawai za a tantance su na aikin Hajjin bana daga babban birnin tarayya Abuja kafin hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta saki ainihin kudin aikin.
Daga Fatima Abubakar.