Shugaba Bola Tinubu ya nada Maryam Shetty a matsayin mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin al’adu da nishaɗi.
Duk da cewa har yanzu ba a bayyana shi a hukumance ba, babban mai goyon bayan shugaban kasa Tinubu , Akinsola Akin ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Tweet din nasa ya karanta kamar haka: “BARKA Shetty, mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan al’adu da nishaɗi.”
Ku tuna cewa an cire sunan Shetty daga jerin sunayen ministoci da kuma wasu mutane biyu da aka nada, Festus Keyamo da Dr Maigari Mahmud.
DAGA FATIMA ABUBAKAR.