A ranar Alhamis din da ta gabata ne hukumar babban birnin tarayya ta cire wasu gine-ginen da ba su dace ba ,da ke dakile hanyar Jabi zuwa Dakibu.
Babban mataimaki na musamman ga ministar sa ido, dubawa da aiwatar da ayyuka na babban birnin tarayya Abuja, Ikharo Attah, wanda ya jagoranci aikin tsaftace yankin Idu, tare da hadin gwiwar sashen kula da ci gaba, jami’an tsaro, hukumar kare muhalli ta Abuja, AEPB, da dukkan hukumomin tsaro da abin ya shafa, duk sun kasance a Idu, da sanyin safiyar yau Alhamis.
Hukumar, ta koka kan yadda mutane ke kutsawa cikin tituna a Abuja, ya kuma ce Ministan ya yi matukar bakin ciki kuma zai ci gaba da kwato hanyar daga hannun baragurbin barayin.
Da take mayar da martani game da korafin mazauna yankin na cewa sun bayar da gudunmawar Naira 10,000 domin hana ma’aikatan babban birnin tarayya cire musu gine-ginen da suka gina ba bisa ka’ida ba.
Hukumar ta ce, “Abin takaici ne, da zarar an sanya wurin da za a cire, sai ku tattara ku koma wani waje. , babu wani dan kasa a yanzu, Ministan babban birnin tarayya, Malam Muhammad Bello, ya gargade mu kan karbar cin hanci daga hannun kowa kuma yau mun zo cire gine-gine-ginen ne ba gudu ba ja da baya.
“Wadanda suka bayar da cin hancin tuni suka yi ta kuka suna kokarin tattara kayansu, zan ba su shawara da kada su ba da cin hanci, kada su sake yin gini a kan titin.
Ya ce ’yan asalin a kodayaushe suna musanta cewa suna sayar musu da fili amma abin da suke sayar musu shi ne filayen noma don haka ya bukaci mazauna Abuja da su daina sayen filaye daga hannun mazauna yankin.
Da ta tofa albarkacin bakinta daya daga cikin wadanda abin ya shafa da ke hawaye ta ce, ta sayi gidan ne a watan Janairun 2023 a kan Naira miliyan 1.4.
“Na sayi wannan gidan ne a watan Janairu, a kan Naira miliyan 1.4, daga hannun tsohon mai gidan da ya koma kasar waje, ba ni da inda zan je, ina wurin aiki sai makwabcinmu ya buga min waya cewa sun rushe gidana.” .
Esara daga jihar Akwa Ibom, ya ce ya shafe shekaru 12 yana zaune a wannan yanki. Ya ce an ruguza tsohon wurinsa don haka ya koma Dakibiu don yin haya.
“Basaraken Dakibiu ne ke siyar da filin, yana sayar da kowane fili akan N150,000 na gida mai daki daya”.
Andrew Ayame, wanda ya ce shi dan jihar Kaduna ne, ya ce ya tattara kayansa tare da kaura da iyalansa kafin zuwiyama’aikatan . Ya yaba wa FCTA da ta ba su isasshen lokaci don ƙaura.
Daga Fatima Abubakar.