Buhari Ya Kori Shugaban NIPC, Saratu Umar

0
18

A yammacin ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da nadin Hajiya Saratu Umar a matsayin babbar sakatariyar hukumar bunkasa zuba jari ta Najeriya, ba tare da bata lokaci ba.

 

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Alhamis mai taken ‘Shugaba Buhari ya sallami Saratu Umar a matsayin shugabar NIPC.

Korar Umar dai na zuwa ne mako guda bayan wani rahoto mai zafi da ya bankado laifuffukan da ke cikin gwamnatin Hukumar.

 

Rahoton ya yi nuni da kalubalen da shugaban NIPC ke fama da shi na “rashin iya aiki da rashin gudanar da aiki.”

Firdausi Musa Dantsoho