Ana Gudanar Da Bikin Rantsar Da Ministoci A Fadar Shugaban Kasa

0
38

Ana gudanar da bikin rantsar da sabbin ministoci 45 da aka nada a babban dakin taro na fadar gwamnatin tarayya, Abuja.

Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda da shugaban kasa Bola Tinubu ya fitar da mukaman wadanda aka nada, wadanda suka hada da tsohon gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike mai kula da ma’aikatar babban birnin tarayya Abuja da Festus Keyamo wanda ke rike da ma’aikatar sufurin jiragen sama.

Dukkan Ministocin 45 sun hallara kuma sune kamar haka; Wale Edun (Ministan Kudi da Gudanarwa na Tattalin Arziki), Adegboyega Oyetola (Ministan Marine & Blue Economy), David Umahi (Ayyuka), Festus Keyamo (Aikin Jiragen Sama da Ci gaban Aerospace), da Betta Edu (Humanitarian Affairs and Poverty Alleviation).

Jerin ministocin Tinubu

Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin dijital, Bosun Tijani
Karamin Ministan Muhalli, Ishak Salaco
Ministan Kudi da Tattalin Arziki, Wale Edun
Ministan harkokin cikin gida, Bunmi Tunji
Ministan wutar lantarki, Adedayo Adelabu
Karamin ministan lafiya da walwalar jama’a, Tunisia Alausa
Ministan Ma’adanai na Kasa, Dele Alake
Ministar yawon bude ido, Lola Ade-John
Ministan Sufuri, Hon. Sa’idu Alkali
Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Doris Anite
Ministan kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, Uche Nnaji
Karamin Minista, Kwadago da Aiki, Nkiruka Onyejeocha
Ministar harkokin mata, Uju Kennedy
Ministan Ayyuka, David Umahi
Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo
Ministan Neja Delta, Abubakar Momoh
Ministar Al’amuran Jin kai da Rage Talauci, Betta Edu
Karamin Ministan Albarkatun Gas, Ekpereikpe Ekpo
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri
Ministan raya wasanni, John Enoh
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike
Ministar fasaha, al’adu da tattalin arziki, Hannatu Musawa
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar
Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle
Karamin Ministan Ilimi, Yusuf T. Sununu
Ministan gidaje da raya birane, Ahmed M. Dangiwa
Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane Abdullahi T. Gwarzo
Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Atiku Bagudu
Mariya Mahmud Bunkure, Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya
Karamin ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli Bello M. Goronyo
Ministan Noma da Abinci, Abubakar Kyari
Ministan Ilimi, Tahir Mamman
Karamin Ministan (Gas), Albarkatun Man Fetur, Hon. Ekperipe Ekpo
Ministan Harkokin Waje, Yusuf M. Tuggar
Ministan lafiya da walwalar jama’a Ali Pate
Ministan harkokin ‘yan sanda, Ibrahim Geidam
Karamin Karafa U. Maigari Ahmadu
Ministan Karafa, Shuaibu A. Audu
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Muhammed Idris
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi
Ministan Kwadago da Aiki, Simon B. Lalong
Ministan harkokin ‘yan sanda, Imaan Sulaiman-Ibrahim
Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Zephaniah Jisalo
Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar muhalli, Joseph Utsev
Karamin Ministan Noma da Abinci, Aliyu Sabi Abdullahi
Ministan Muhalli da Kula da Muhalli, (Kaduna)

Firdausi Musa Dantsoho