Mako guda kafin zaben 2023, rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Adamawa a ranar Juma’a, ya dauki wani salo, yayin da kwamitin zartarwa na karamar hukumar Yola ta Kudu APC ta dakatar da ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar, Aisha Dahiru Ahmed wadda aka fi sani da Binani. saboda zargin da ake yi mata na haifar da rarrabuwar kawuna, da tada rikici a cikin jam’iyyar.
An bayyana dakatarwar ne a cikin wata wasika da kwamitin APC ta rubuta.
Wasikar mai dauke da kwanan watan 17 ga watan Fabrairu mai take: ƙudirin kwamitin zartarwa na ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a kan Sanata A’isha Dahiru Ahmed ( ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC) tana ɗauke da sashe kamar haka:
“Mu ‘yan kwamitin zartarwa na kananan hukumomi da wadanda aka sanya wa hannu a taron da aka yi a Sakatariyar Jam’iyyar ta Karamar Hukumar da ke Yola a ranar 17 ga Fabrairu, 2023, mun karba tare da duba koke kan Sanata Aishatu Dahiru Ahmed (yar takarar Gwamnan Jihar APC), takardar gayyata, da kuma shawarar kwamitin ladabtarwa na rashin fitowar ta da kuma kare kanta kan zargin da Auwal Hammanadama Bawuro ya shigar.
“Saboda haka, bisa ga abin da muka ambata, kwamitin zartarwa ya yanke shawarar dakatar da Sanata Aishatu Dahiru Ahmed daga jam’iyyar kuma ta haka ne aka dakatar da ita na tsawon watanni shida (6) daga 17 ga watan Fabrairu, 2023, daga APC.”
Daga Safrat Gani