ASUU TA ZARGI SHUGABA BUHARI,KUMA TA CI ALWASHIN BA ZATA SAKE ZAMA DA GWAMNATIN TARAYYA BA.

0
52

 

A Yayin da ‘yan Nijeriya ke nuna bacin ran su kan tallafin dala miliyan 1 da shugaban kasa muhammadu Buhari ya bayar ga kasar Afghanistan,hakan ya faru ne a daidai lokacin da malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yajin aiki.

Kungiyar malaman sun yi Allah wadai da tallafin da shugaban kasar ya baiwa kasar larabawa domin biyan bukatun al’ummar kasar Afghanistan da suka hada da mata da kananan yara.

Wannan bayanin na kunshe ne a wani sako da suka wallafa a shafin twitter a ranar juma’a ta shafin kungiyar ta ASUU,inda suka bayyana cewa matakin shugaban kasar ya zo ne a dai dai lokacin da kungiyar ke bukatan a cika mata yarjejeniyar ta.

ASUU a sakon da ta wallafa,kuma ta sha alwashin ba za ta sake tattaunawa da Gwamnatin Tarayya ba har sai an cika mata burin ta.

Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC) Hussain Brahim Taha,cikin wata sanarwa da ya fitar,ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya bayar da kudin ne saboda matsalar jin kai da ake fama da shi a Afghanistan.

 

Daga Fatima Abubakar.