An gaya wa ‘yan Najeriya da su yi watsi da tsohon takardun Naira daga bankuna.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar da wannan umarni ga ‘yan Najeriya, inda ya dage kan cewa tsofaffin takardun kudi zasu daina zama amfani kafin ranar 31 ga watan Janairu kamar yadda aka tsara tun farko.
Mataimakiyar darakta mai kula da harkokin kudi, Dr Rekiyat Yusuf, ta bayyana hakan a Lokoja, jihar Kogi, a ranar Alhamis, a yayin taron wayar da kan jama’a maza da mata ‘yan kasuwa game da sake fasalin kudin naira.
Ta ce za a sanya takunkumin da ya dace kan duk wani banki da aka samu yana raba tsofaffin takardun kudi ga kwastomomi daga yanzu.
Don haka Babban Bankin Najeriya ta umurci abokan huldar su da su kai rahoton duk wani banki da har yanzu yake raba tsofaffin takardun kudi a kan kantuna ko kuma ta hanyar ATM na Automated Teller Machine zuwa babban bankin.
Dr Rekiyat ta kuma bukaci ‘yan kasuwa da su ci gajiyar damar na wa’adin ranar 31 ga watan Junairu ta hanyar ziyartar bankuna domin musanya tsofaffin takardun kudi zuwa sababbi.
“Babu wani dalilin da zai sa bankunan su ci gaba da ajiye na’urorinsu na Automated Teller Machines da tsofaffin takardun kudi kamar yadda bankin Apex ya samar da isassun bayanan da aka tsara don rabawa jama’a. Duk bankin da aka kama za a sanya shi ya fuskanci hukuncin da ya dace”, in ji ta. .
A martanin da ta mayar wa wani abokin ciniki kan yadda ake ci gaba da raba tsofaffin takardun kudi na Naira ta hanyar ATMs, Dr Yusuf ta ce, “Idan bankuna suka ba ku tsofaffin takardun kudi, sai ku ki amsa sannan ku mayar da su bankuna, ku kawo mana rahoton bankunan nan da nan domin daukar matakin da ya dace, mun baya su isassun sabbin kuɗaɗen don rabawa don maye gurbin tsofaffin waɗanda ke yawo.
Daga:Firdausi Musa Dantsoho
ReplyForward
|