CDS ya jinjinawa kwamitin da ta wanke sunan Soji Kan zargin zub da ciki a Arewa maso gabas.

0
7

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Janar Christopher Gwabin Musa ya jinjinawa kwamitin bincike na musamman mai zaman kansa kan take hakkin bil’adama a yankin Arewa maso Gabas bisa wanke sojojin Najeriya daga tuhume-tuhume da kungiyar agaji ta Red Cross ta yi. (ICRC) da Reuters game da zarge-zargen zubar da ciki da kuma wasu laifuka a Arewa maso Gabas.

Wannan sanarwan Mai dauke da kwanan wata 9 ga watan Nuwamba 2024, ya fito ne dauke da sa hannun Daraktan labarai na helkwatar Soji Brigadier Janar Tukur Gusau

Idan dai za a iya tunawa, rahoton kwamitin ya bayyana cewa, zargin da ake yi na zubar da ciki, gallazawa, fyade da kuma kisan gilla da ake yi wa AFN, karya ne.

Don haka CDS ya  yabawa kwamitin mutum 7 da Mai Shari’a Abdu Aboki (rtd) ya jagoranta bisa jajircewar da suka yi wajen gudanar da ayyuka masu inganci tun bayan kaddamar da hukumar a watan Maris 2023 da hukumar kare hakkin bil’adama ta Najeriya ta yi.

Janar Musa na fatan yin amfani da wannan dama domin jaddada aniyar rundunar sojin Najeriya na kare hakkin dan adam da kudurin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

A cewar sa “ba wani zarge-zargen karya da zai janye hankalin AFN daga aiwatar da aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi na kare martabar yankunan kasa”

 

Daga FATIMA Abubakar.