Jami’an yan sandan Nijeriya sun kama dakataccen shugaban hukumar leken asiri ta intelligence response team(IRT)DCP Abba kyari.
An kama shi ne da wasu mutum hudu ranar litinin 14 ga faburairu 2022 a bisa zargin alaka da miyagun kwayoyi.
Kamen dai ya zo ne sa’o’i bayan da hukumar yaki da fataucin miyagun ta kasa NDLEA ta ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin alaka da miyagun kwayoyi.
Ana kuma ci gaba da binciken yan sandan bayan da hukumar binciken manyan laifuka ta kasar amurka FBI ta tuhume shi da laifin zamba da ya shafi wani fitaccen jarumin Instagram Raymond Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Wani kwamiti na musamman da IGP Usman Alkali ya kafa don bincika rahoton,wanda kuma ya mika shi ga babban mai shari’an tarayya kuma ministan sharia Abubakar Malami domin samun shawarwarin sharia.
Hukumar kula da ayyukan yan sandan(PSC)ta baiwa yan sandan wa’adin makonni biyu domin kammala bincike akan abinda ya shafi kyari.
BY Fatima Abubakar.