Da dumi-dumin ta Hukumar zabe mai zaman kanta ta dage zaben Gwamnoni da ‘yan majalisun jiha da mako guda.

0
42

Hukumar zabe mai zaman kanta ta dage zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha da aka shirya gudanarwa a ranar 11 ga watan Maris da mako guda.

Yanzu dai za a gudanar da zaben ne a ranar 18 ga Maris, 2023.

Wani Kwamishinan Zabe na Jihar da ya zanta da wakilin punch  bisa sharadin sakaya sunansa ya tabbatar da matakin.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu da kwamishinonin sa sun yi wata ganawar sirri kan zaben gwamna. An fara taron ne da karfe 7 na yammacin Laraba ta yau.

 

Cikakkun bayanai daga baya…

 

Daga Fatima Abubakar.