Da DUMI DUMIN TA:Daruruwan Shaguna Sun Kone a Monday Market da ke Maiduguri, yayin da wata mummunar gobara ta auku a yau Safiyar Lahadi.

0
151

Wata gobara ta kone kantuna da dama dauke da kayayyaki na miliyoyin naira a babbar kasuwar Litinin mai suna MMM.

Majiyoyi sun ce lamarin wanda ya faru da misalin karfe biyu na safiyar Lahadi, bai samu asarar rayuka ba, yayin da jami’an kashe gobara suke fafatawa don kashe gobarar.

An ba da rahoton cewa daruruwan shaguna sun kone kurmus yayin gobarar.

Kawo yanzu dai ba a gano musabbabin tashin gobarar ba domin ta faru ne da daddare a lokacin da kasuwar ta kasance a rufe.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, jami’an kashe gobara na ci gaba da kokarin kashe gobarar, yayin da ‘yan kasuwa da masu goyon bayansu suka yi dafifi a wurin da misalin karfe 7 na safiyar  yau Lahadi.

 

Daga Fatima Abubakar.