DA DUMI DUMIN TA;Gwamna A.A Sule na jahar Nasarawa, ya rasa dan sa Alhaji Hassan A Sule da safiyar yau.

0
39

Gwamnan Jihar Nasarawa, Engr Abdullahi A. Sule ya yi rashin dansa, Alhaji Hassan AA Sule da safiyar Juma’a ta yau.

An tattaro cewa Hassan ya rasu ne bayan gajeriyar jinya. A halin da ake ciki kuma, an fara zaman  ta’aziyyar rasuwar dan gwamnan.

A cikin sakon ta’aziyya da Mawallafin Eggonnews, Matthew Kuju ya sanya wa hannu a Lafia baban birnin jahar da misalin karfe 5:30 na safe, ya ce: “Yana matukar bakin cikin rasuwar na Hassan. Babu shakka, yana da zafi ace ka rasa dan ka har abada, amma Allah shi ke badawa kuma shi ya dauki abin sa.

“Muna rokon Allah Ya daukaka shi a cikin salihai, kuma Ya ba shi Aljannah Firdausi, kuma Allah Ya ba wa iyalan sa  karfin guiwar jure wannan rashi mai raɗaɗi.

A wani sako makamancin haka, dan majalisar mai wakiltar mazabar Lafia ta Arewa a majalisar dokokin jihar Nasarawa Hon. Barr. Muhammed Ibrahim Alkali ya ce ya samu matukar kaduwa da rasuwar Dan Mai Girma Gwamnan Jihar Nasarawa Alh. Hassan Abdullahi Sule.

A cikin sakon ta’aziyya ga Maigirma Gwamnan Jihar Nasarawa, Mai Girma Engr. Abdullahi A. Sule, dan majalisar ya bayyana rasuwar dan gwamnan a matsayin babban rashi ba ga jihar Nasarawa kadai ba har ma da kasa baki daya.

Hon. Alkali ya yi addu’ar Allah ya jikan mamacin ya gafarta masa dukkan kurakuran sa  kuma ya ba shi Aljanatul Firdaus.

 

Daga FatimaAbubakar