An tsince yarinya ‘yar shekaru 13 a Maiduguri,yayin da ta bace a Kano.

0
13

Wata yarinya ‘yar shekara 13 da ta bace makonni biyu da suka gabata a Kaduna amma an tsince ta a jahar Borno.

An gano yarinyar tana yawo a tashar Borno Express Corporation da ke Maiduguri inda aka mika ta ga ‘yan sanda.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Sani Kamilu, ‘yan sandan sun gudanar da bincike na gaskiya domin gano dangin yarinyar.

Kamilu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Maiduguri yayin da yake mika yarinyar ga mahaifinta, ya ce babban jami’in tsaro na tashar, Ahmadu Buba ne ya kawo ta ga ‘yan sanda.

“Ta kasance karkashin kulawar DPO na ofishin ‘yan sanda na Metro, CSP Hadiza Musa Sani inda aka fara kai rahoton lamarin kimanin makonni biyu da suka wuce.

“Bayan bincike mai zurfi, mun gano inda iyayenta suke a Kaduna wadanda yanzu haka suke nan domin karbar ta a hukumance.”

Mahaifin, Ado Usman, ya ce yarinyar da ke da “matsalar runhanai”, ta yi batan dabo sau da yawa a baya.

“Wannan ba shi ne karon farko ba, akwai lokacin da ta hau keke aka same ta a kusa da Kano.

“Ta kasance tana tashi a firgice a cikin dare tana cewa wani yana kiranta ta biyo shi a wani wuri; muna iyakacin kokarinmu kuma za mu ci gaba da yi mata addu’a,” in ji Usman.

Ya yabawa ‘yan sanda da duk wadanda suka taimaka wajen ganowa da kuma tabbatar da tsaron yarinyar.

Yarinyar ta kasance cikin rashin jituwa lokacin da aka tambaye ta ta bayyana yadda ta yi tafiya daga Kaduna zuwa Maiduguri.

 

Daga Fatima Abubakar.