Dage zabe na iya shafar fara kidayar 2023 – NPC

0
64

Fara kidayar gidaje da yawan jama’a na kasa na shekarar 2023 da aka shirya tun a ranar 29 ga watan Maris mai yuwuwa dage zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihohi zai iya shafarsa.

 

Hakan na zuwa ne a cewar shugaban hukumar kidaya ta kasa, Malam Nasir Kwarra, wanda ke magana a wani taro da wakilin gidauniyar kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya a Abuja.

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tsara gudanar da zabukan jihohin a ranar 11 ga watan Maris daga bisani ta dage zaben zuwa ranar 18 ga watan Maris.

 

Ko da yake ba a kayyade takamaiman ranar da za a fara aikin ba, Mista Kwarra ya shaida wa manema labarai cewa zai tuntubi shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ranar da ta dace da kidayar jama’a.

 

A nata bangaren, wakiliyar asusun kula da yawan al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya, Ulla Mueller, ta yi alkawarin tallafawa UNFPA wajen tabbatar da nasarar aikin.

 

Yayin da take nanata mahimmancin aikin na cimma burin ci gaba mai dorewa, Mueller ta bayyana cewa gudanar da binciken bayan kidayar zai kuma ba da tabbaci ga kidayar.

 

Don tallafawa binciken bayan ƙidayar, UNFPA ta gabatar da manyan kwamfutoci goma sha shida don gudanar da binciken bayan ƙidayar.

 

Daga: Firdausi Musa Dantsoho