Duk da Umarnin da Gwamnan Gombe ya bayar, ‘Yan Sanda sun ki wargaza wuraren binciken ababen hawa, Direba sun koka ga lamarin

0
80


Duk da umarnin da gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayar na a gaggauta rusa duk wuraren binciken jami’an tsaro a jihar, binciken News Point Nigeria ya nuna cewa har yanzu wuraren binciken ‘yan sanda na ci gaba da gudana a duk fadin jihar.

Idan za’a iya tunawa a ranar 6 ga watan Maris, gwamnan jihar a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Meshack Lauco ya sanyawa hannu, ya bayar da umarnin rusa dukkanin wuraren binciken ‘yan sanda dake Gombe cikin gaggawa.

A cewar sanarwar, an cimma matsayar ne biyo bayan tuntubar da ta dace da shugabannin hukumomin tsaro na jihar. Gwamnan ya bukaci ‘yan kasar da su bayar da hadin kai ga wannan umarni domin samar da zaman lafiya da tsaro a jihar, ko da a samu ci gaba.

Sanarwar ta kara da cewa wuraren binciken da ke kan iyaka da jihohin da ke makwabtaka da su “za su ci gaba da kasancewa a wurin kuma za a rufe su ne kawai don zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 12 na dare zuwa karfe 6 na safe,” in ji sanarwar.

Binciken News Point Nigeria, ya nuna cewa akwai sama da  wuraren binciken ‘yan sanda 43 da ke ci gaba da aiki sa’o’i 24 a rana a fadin kananan hukumomi 11 da masarautu 14 da ke jihar.

Wakilin news point, da ya je daukacin kananan hukumomin jihar cikin kwanaki uku, ya gano cewa, 5 ne kacal daga cikin 48 da aka soke a fadin jihar baya aiki bayan umarnin gwamna.

 

Wuraren binciken ababen hawan guda biyar da aka daina aiki su ma wuraren bincike ne da ke kusa da gidan gwamnati da kuma cikin yankunan babban birnin jihar.

 

A wajen babban birnin, akwai wuraren bincike guda 16 daga Shomgom zuwa Billiri, zuwa Akko, zuwa babban birnin jihar, zuwa Kwami zuwa Funakaye zuwa Nafada.

 

Haka kuma akwai wuraren cak guda 11 daga Dukku zuwa babban birnin jihar zuwa Yamaltu Deba, yayin da akwai wuraren cak guda 18 daga Balanga zuwa Kaltungo zuwa babban birnin jihar har zuwa Wuro Bongu.

 

Da yake zantawa da newspoint, wani direban motar bas din ‘yan kasuwa, Haruna Dan Bauchi, ya ce ‘yan sandan ba za su wargaza wuraren binciken ba saboda ‘yar cin hancin da suke samu daga direbobin ‘yan kasuwa da masu zaman kansu.

 

“Wannan hanyar ta Gombe hanya ce mai cike da cunkoso ga matafiya musamman ‘yan siyasa da ’yan kasuwa da ke zuwa Kano, Kaduna daga gabas mai nisa ko makwaftan kasashen Afirka. Su kuma wadannan jami’an tsaro suna samun makudan kudade, to ta yaya kuke tsammanin za su wargaza wadannan wuraren binciken. Ba za su yi ba.”

 

Ya kara da cewa “Gwamnan ya yi wa kungiyoyinmu alkawarin cewa zai duba wadannan batutuwan wuraren binciken ababen hawa kuma mun yi alkawarin za mu zabe shi a ranar 18 ga Maris, amma da ‘yan sandan suka ki bin umarnin, wannan yarjejeniya baza ta yiwu ba.”

 

Da yake mayar da martani kan zargin, wani dan sanda a daya daga cikin wuraren binciken ababen hawan, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya musanta cewa ‘yan sandan sun ki amincewa da hakan ne saboda ‘dan abun da suke samu daga matafiya da direbobi.

 

“Akwai manyan barazanar tsaro a wadannan hanyoyin, ban ma fahimci dalilin da ya sa gwamnan ya ce mu bar aiki ba, komai siyasa ce a kasar nan, don kawai yana son a sake zabe shi. Muna nan don kare matafiya – ba don wani abu ba. ”

 

 

 

Da yake mayar da martani kan lamarin, babban daraktan hulda da manema labarai na gwamnan, Ismaila Uba Misilli, ya ce gwamnati ba ta da masaniyar kan kin bin umarnin da ‘yan sanda suka yi amma zai binciki lamarin sannan ya dawo ga jaridar.

 

Daga :Firdausi Musa Dantsoho