Gidauniyar ba da tallafi tayi wani yunkuri na karfafa kiyaye dukkan al’adun ’yan asalin Abuja
Shugabar gidauniyar, Dakta Jumai Ahmadu a lokacin da take gabatar da taron na biyu a fannin tattalin arziki kan horar da sana’o’in gargajiya a jiya, ta ce kungiyar tare da wasu hukumomi sun zabo wasu ‘yan asalin kowace karamar hukumar domin horas da su tufafin gargajiya da sauransu.
Ta bayyana cewa atisayen na da nufin taimaka wa harshe da al’adun ’yan asalin kasar don kada su gushe a nan gaba.
Ahmadu, wacce ta samu wakilcin manajan aikin, Onoja Arome, ta ce shirin zai kuma taimakawa mazauna babban birnin tarayya Abuja wajen karfafa tattalin arzikinsu, samar da ayyukan yi da kuma rage rashin daidaito.
Ta bayyana cewa gabatar da tuta na kashi na biyu na shirin wanda ya mayar da hankali kan sanya tufafin gargajiya na mazauna asali an fara gudanar da shi ne a shekarar 2022.
Kashi na biyu, ta ce za ta samar da wayar da kan jama’a kan hanyoyin tattalin arziki don inganta ayyukan al’adu da kuma kara amfanar da al’adu.
A cewarta, “Helpline Foundation tare da tallafi daga gidauniyar Macarthur ta hanyar cibiyar kare hakkin dan adam da ilimin jama’a ta kaddamar da ayyukan ci gaban tattalin arzikin cikin gida ga mazaunan FCT na asali don karfafa tattalin arzikin jama’a, samar da ayyukan yi da rage rashin daidaito.
“A karshen wannan aikin, tsare-tsaren mu na dorewa shine sa ido kan ci gaban da aka samu, da alkawurran da hukumar da ke da alhakin aiwatarwa da kuma bayar da kanmu ga kiransu a kowane lokaci don ba da shawara.”
A cikin jawabinsa mai taken, ‘Local Economic Development’ Manajan aikin, Onoja Arome ya ce gidauniyar za ta horar da marasa galihu kusan 100 a rukunin B, na Canjin Kwarewar Gargajiya.
Ya ce za a fara horas da wadanda za su ci gajiyar shirin ne daga watan Fabrairu zuwa karshen watan Afrilu, 2023.
Daga Fatima Abubakar.