Girgizar kasa mai karfin awo 5.6 ta afku a lardin Malatya da ke kudancin kasar Turkiyya
An kama ma’aikatan gine-gine kan rugujewar gine-gine a girgizar kasar na wannan watan
A yau ne wata girgizar kasa ta sake afkuwa a kasar Turkiyya, inda ta kashe mutum daya tare da raunata wasu 69, tare da rugujewar gine-gine da tuni suka lalace – makonni uku bayan wata mummunar girgizar kasa ta barnata kasar tare da kashe mutane 48,000.
Hukumar kula da bala’o’i ta kasar Turkiyya ta sanar da cewa girgizar kasar mai karfin awo 5.6 ta afku a garin Yesilyurt da ke lardin Malatya da ke kudancin kasar Turkiyya.
An kubutar da wani uba da ‘yarsu daga karkashin baraguzan ginin bene mai hawa hudu kuma aka dauke su zuwa motar daukar marasa lafiya a kan shimfida. Magajin garin Yesilyurt, Mehmet Cinar, ya ce ma’auratan sun shiga cikin ginin da ya lalace ne domin tattara kaya.
Hotunan ban mamaki sun nuna cewa tuni gine-gine da suka lalace suka ruguje cikin tarkace a kan titunan Malatya biyo bayan girgizar kasar, yayin da masu aikin ceto suka zakulo baraguzan ginin wani gini da ya kife kan wasu motoci da aka faka.
Malatya na cikin larduna 11 na Turkiyya da girgizar kasa mai karfin awo 7.8 ta yi barna a yankunan kudancin Turkiyya da arewacin Siriya a ranar 6 ga watan Fabrairu. a Turkiyya.
Daga Fatima Abubakar.