Daga Yunusa Isa, Gombe
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya sanya hannu kan ƙudurin kasafin kuɗin 2024 na fiye da Naira biliyan 208.
Da yake jawabi yayin rattaba hannun a zauren majalisar Zartaswar jihar dake gidan gwamnati, Gwamna Inuwa yace kaso 58 cikin ɗari na kasafin zai tafi ne ga manyan ayyuka, yayin da kaso 42 cikin ɗari za a kashe su a harkokin gudanarwa na yau da kullum.
Yace kasafin ya fi bada fifiko ne ga buƙatun ci gaban jama’a, don haka ɓangaren manyan ayyuka ya samu kaso mafi tsoka.
Da yake bada tabbacin aiwatar da kasafin yadda ya kamata, gwamnan ya yabawa majalisar dokokin jihar bisa yadda ta hamzarta amincewa da kasafin.
Ya kuma yaba da haɗin kan dake tsakanin majalisar da ɓangaren zartaswa, yana mai bada tabbacin kyautatuwar alaƙa tsakanin rukunan gwamnati uku don hidimtawa al’ummar jihar yadda ya dace.
Da yake jawabi gabanin sanya hannu kan kasafin kuɗin, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar ta Gombe Hon. Abubakar Muhammad Luggerewo, yace karɓar ƙudurin kasafin ke da wuya majalisar ta shiga aiki akansa gadan-gadan don tabbatar da amincewa da shi a kan lokaci, wanda yace sun yi hakan ne cikin dan lokacin da bai wuce makonni biyu ba.
Ya yabawa gwamnan kan yadda ya baiwa buƙatun al’ummar Jihar Gombe fifikon a kasafin, tare da rage kuɗaɗen da ake kashewa a harkokin mulki.
Abubakar Luggerewo ya ƙara da cewa majalisar ta yanke shawarar yin ƙari a adadin kasafin, daga fiye da Naira biliyan 207 da gwamnan ya gabatar mata, zuwa fiye da Naira biliyan 208 bisa la’akari da wasu muhimman ayyuka da suka shafi jama’a, yana mai cewa sun ɗauki matakin ne don amfanin Jihar Gombe baki ɗaya.
Da yake yabawa ma’aikatar kasafi da tsare-tsare ta jihar kan sauwake yanayin kasafin kuɗin, Luggerewo ya yabawa kwamitin majalisar kan kasafin kudi bisa jajircewarsa da ya kai ga hamzarta tantancewa da amincewa da kasafin.