Gwamnan jihar Kuros Riba, Sanata Bassey Otu ya bayar da umarnin haramta duk wani babura na kasuwanci a cikin babban birnin Calabar.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Emmanuel Ogbeche ya fitar ranar Laraba, inda ya bayyana cewa haramcin ya biyo bayan shawarwarin da ya dace da shugabannin tsaro a jihar.
A cewar sanarwar, masu son yin amfani da babura don samun abin dogaro da kai, an takaita su ne kawai ga lungunan da ke nesa da tsakiyar birnin.
Gwamnatin jihar ta yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana karya dokar za a kwace babur din tare da hukunta wanda ya aikata laifin.
Sanarwar ta kara da cewa “Gwamnan, Sanata Bassey, bayan tuntubar manyan jami’an tsaro a jihar ya ba da umarnin haramta duk wani babura na kasuwanci a cikin Calabar.”
“Wadanda ke son yin amfani da babura don samun kudi an takaita su ne kawai ga lungu da sako da ke nesa da tsakiyar gari.”
Gwamnatin jihar ta kuma yi gargadin a kan barnatar da dukiyoyin al’umma kamar fitulun titi, fitulun ababan hawa, ta shawarci masu aikata laifuka da su kau da kai domin masu laifi za su fuskanci fushin doka.
Firdausi Musa Dantsoho