Attajirin Afirka ta Kudu ya maye gurbin Dangote a matsayin wanda ya fi kowa arziki a Afirka

0
57

Shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote,ya rasa matsayinsa  ya zama na biyu a cikin jerin attajirin da suka fi kowa kudi a Afirka bayan da dukiyarsa ta ragu da kashi 20.7 cikin 100.
Hakan ya faru ne sanadiyar rage darajar Naira da babban bankin Najeriya (CBN) ya aiwatar, a cewar mujallar Forbes Billionaire Ranking da aka fitar jiya.

Yanzu dai Dangote ya zama na biyu a Nahiyar bayan hamshakin attajirin nan na Afirka ta Kudu, Johann Rupert ya zama a matsayi na daya a jerin.

CBN dai ya karya darajar Naira, wanda hakan ya sa darajar ta ragu da kashi 40.5 cikin 100.

Arzikin Dangote ya ragu da dala biliyan 2.80 zuwa dala biliyan 10.7, daga dala biliyan 13.5, abin da ya kawo cikas ga kasancewan shi mafi arziki a karon farko tun shekarar 2008, lokacin da ya fara fafata a kan mujallar Forbes Billionaire Index.

Rupert ya zama mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka bayan da dukiyarsa ta karu da dala biliyan 1.3 daga dala biliyan 10.7 zuwa dala biliyan 13.5.

Firdausi Musa Dantsoho