Hukumar tsaro a jihar Legas da ta Rapid Squad Response sun rufe cibiyar taron Havillah.
Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar Legas Gbenga Omotosho ya bayyana a yau asabar cewa Gwamnatin Legas za ta yi bincike kan yadda aka yi anfani da man fetur a matsayin abin tunawa a wurin biki.
Omotosho ya ce ko shakka babu matakin na tattare da hadari kuma zai iya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi,kuma hakan ya sabawa dukkan matakai na tsaro a irin wadannan wuraren.
A cewar sa ,Gwamnatin jihar Legas ta hannun Hukumar ta tsaro za ta tabbatar da cewa dukkan bangarorin sun yi la’akari da lamrin .
Tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Legas har ma da masu ziyara ya kasance babban fifiko ga Gwamnati.
Saboda haka,muna ba da shawarar cewa a guji ayyukan da za su iya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.
Daga Fatima Abubakar