Gwamnatin tarayya Ta Bada Umarnin Rufe Makarantun polytechnic Kan Zabe

0
48
A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta umurci dukkanin makarantun polytechnic na kasar nan da su rufe har sai bayan babban zabe mai zuwa.
 Wannan ci gaban ya zo ne mako guda bayan fitar da irin wannan umarnin na rufe dukkan Jami’o’in kasar.
 News Point Nigeria ta rahoto cewa, umarnin yana kunshe ne a cikin wata takardar da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta fitar, inda ta umurci Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Kasa (NBTE), Farfesa Idris Bugaje da ya yi magana da masu kula da polytechnics.
 Wasikar mai dauke da sa hannun Mista I. O Folorunsho, ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu mai kwanan wata 10 ga watan Fabrairu, ta samu ne daga manema labarai a Abuja ranar Litinin.
 ” Bisa la’akari da damuwar da ake nunawa a kan tsaron ma’aikata da dalibai da dukiyoyin makarantun mu, Ministan Ilimi Adamu Adamu, ya yi shawarwari da hukumomin tsaro da abin ya shafa, ya bayar da umarnin a rufe dukkan makarantun Polytechnic.
 ” Kuma za a dakatar da ayyukan ilimi tsakanin Laraba 22 ga Fabrairu zuwa Talata.  Maris 14, 2023, ”wasikar ta karanta.
 Ministan ya bukaci shugaban NBTE ya sanar da abubuwan da ke sama ga dukkan cibiyoyin da ke karkashin ayyukan sa.
 Daga: Firdausi Musa Dantsoho