Gwamnatin jihar Zamfara zata raba kayayyakin abinci ga gidajen mabukata dubu dari biyu 200,000, zata samarda motocin sufuri da kuma jigilar daliban firamare kyauta zuwa makaranta.
Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar M. Nakwada ya ce, a wani bangare na kudurin da majalisar ta zartaswa ta cimma, mabukata dubu dari biyu (200,000) a jihar zamfara za su amfana da kayan abinci a matsayin daya daga cikin hanyoyin magance radadin cire tallafin man fetur daga gwamnatin tarayyar Najeriya.
A cewarsa, za’yi la’akari da wasu da suka cancanta daga cikin ma’aikatan gwamnatin jihar Zamfara don yin irin wannan karimcin garesu a cikin tsarin da ya dace na shirin rage radadin da ake ciki.
Hakazalika majalisar zartaswar ta amince da samar da motocin bas guda hamsin (50) nan take don farawa da kuma samarda wasu Motoci guda 10 masu daukar mutane 52 kirar Macopolo don rage matsalolin sufuri ga daliban jihar Zamfara.
Bugu da kari kuma, daliban makarantun firamare kuma, za su amfana da sufuri kyauta .
Daga Fatima Abubakar.