FCT: Za mu dawo da babban tsarin Abuja, mu ruguza duk wasu haramtattun gine-gine –in ji Wike

0
32

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Mista Nyesom Wikle ya ce zai rusa duk wasu haramtattun gine-gine a babban birnin tarayya Abuja a wani bangare na kokarin dawo da babban tsarin Abuja.

Wike ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin da ta gabata, inda ya bayyana shirin gajerun zango, matsakaita, da kuma na dogon lokaci na yin garambawul ga babban birnin tarayya Abuja da kuma mayar da ita a cikin manyan biranen duniya.

A matsayinsa na sabon sheriff a garin, ya ce: “Ba za a yi kasuwanci ba kamar yadda aka saba. Masu karkatar da babban tsarin Abuja: idan ka yi gini a inda bai kamata ba, ginin zai ruguje.

“Idan ka gina a kan koren wuri toh ka sani za mu rushe. Waɗanda aka ware aka ƙi raya su, za mu soke irin waɗannan filayen mu sake raba su ga waɗanda suke shirye su raya su.

“Wadanda ba sa biyan hayar gida, ba za mu sanar da su yin hakan ba, amma ba zan gaji da sanya hannu kan takardar janyewa ba.

“Gine-ginen da ba a kammala ba wadanda suka zama mafakar masu aikata laifuka gwamnati za ta kwato su kuma ta yi amfani da su sosai.”

Ministan ya kara da cewa gwamnati ba za ta kara lamuntar yadda kasuwanni da wuraren ajiye motoci ke yi a bakin titi ba.

Ya ce mutanen da ke sayar da kayayyaki  a karkashin inuwa ta gefen titi, wuraren shakatawa na motoci da kuma tashar bas ba za a daina la’akari da su ba, ya ce sun kasance wani bangare na kalubalen tsaro a babban birnin tarayya Abuja.

“Idan kana da ɗan’uwa, ’yar’uwa, ko kawu da ke cikin ɗaya cikin waɗannan, don Allah ka gaya masa cewa lokaci ya yi. Manufar ita ce a tsaftace Abuja da kuma samar da tsaro ga kowa da kowa,” inji shi.

Ya kuma ce za a yi kokarin karfafa sharar gida da kuma dawo da dukkan fitulun ababen hawa domin tsaftace birnin.

Ya kara da cewa, za a hana masu babura da masu tuka keke a cikin birnin tare da kawo karshen kiwo a cikin babban birnin kasar.

“Za mu tuntubi masu ruwa da tsaki, ’yan kasa, da makiyaya domin magance wasu matsalolin da suka hada da kiwo a fili.

“Za mu samar da wasu hanyoyi don rage radadin jama’a, musamman wadanda ba su da motoci masu zaman kansu.

“Za mu dawo da zirga-zirgan motocin Gwamnati don inganta hanyoyin zirga-zirgar jama’a, don haka, wanda ke kula da harkokin sufuri dole ne ya kiyaye tarihinsa mai tsabta,” in ji shi.

Ya ce za a mayar da hankali ne kan samar da ababen more rayuwa, tare da daukar ayyuka daya lokaci daya domin dawo da martabar birnin.

Ministan ya ce za a kuma kara fadada ayyukan ci gaba zuwa kananan hukumomin shida a wani bangare na dabarun rage cunkoso a birnin.

Ya kuma ce za a toshe duk wata barakar kudaden shiga domin a samu damar tattara abubuwan da ake bukata domin bunkasa ababen more rayuwa a babban birnin tarayya Abuja.

Dangane da batun tsaro, Wike ya ce zai yi aiki tare da dukkan hukumomin tsaro a babban birnin tarayya Abuja tare da samar musu da kayan aiki  da suka dace don kawar da duk wasu masu aikata laifuka a birnin.

A cewarsa, ya kamata a ce babban birnin tarayya Abuja ya kasance birni mafi aminci a kasar, amma duk da haka, birnin ya daina zaman lafiya.

“Za mu samar wa jami’an tsaro kayan aiki da  suka dace sannan kuma ba za mu so jin wani uzuri ba. Abin da muke son gani shi ne sakamako.”

Wike ya kuma yi alkawarin yin la’akari da ‘yan asalin ƙasar a cikin nadin siyasa da nufin ɗaukar kowa da kowa.

Ya nemi goyon bayan duk masu ruwa da tsaki ciki har da kafafen yada labarai don dawo da kwarin gwiwar jama’a kan yunkurin gwamnatin shugaba Bola Tinubu domin baiwa mutane rayuwa mai inganci.

 

Daga Fatima Abubakar.