Gwamnonin APC Sunyi Zaman Sirri, Ganduje Zai Iya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar

0
17

A yammacin ranar Laraba ne gwamnonin jam’iyyar APC suka gudanar da taro a bayan fage, domin tattaunawa kan halin da jam’iyyar ke ciki, bayan murabus din shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu; da sakataren kasa, Sanata Iyiola Omisore.

Su biyun sun sauka ne a ranar Litinin, inda hakan ya bawa mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa (Arewa), Sanata Abubakar Kyari,damar kasancewa a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Wata majiya mai tushe ta shaidawa News Point Nigeria cewa, taron na iya kuma sanya tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.

Majiyar ta kara da cewa, shugaba Bola Tinubu yana son amintaccen kuma na kusa da shi ne ya rike harkokin jam’iyyar kuma duk da cewa wasu daga cikin ’yan shugaban kasar na yi wa wannan ra’ayin harbawa, shi kansa shugaban kasar ya gamsu cewa tsohon gwamnan jihar Kano ne ya dace da aikin.

An kuma tattaro cewa, a safiyar yau, Ganduje ya yi ganawar bayan fage da shugaban kungiyar gwamnonin jihar Imo, Hope Uzodinma, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq da gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun.

Jaridar ta samu labarin cewa Ganduje ya amince ya sadaukar da burinsa na minista domin yin aiki don amfanin jam’iyyar da kasa baki daya.

Wadanda suka halarci taron da Gwamna Uzodinma ya jagoranta sun hada da gwamnonin Ekiti, Ebonyi, Niger, da Benue.

Sauran sun hada da gwamnonin Kaduna, Legas, Yobe, Katsina da Kebbi, da kuma mukaddashin gwamnan jihar Ondo.

In kuntuna Kyari ya gaji Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar bayan taron kwamitin ayyuka na kasa (NWC) a Abuja ranar Litinin.

Da yake zantawa da manema labarai bayan taron na NWC, Kyari ya sanar da murabus din Adamu da Omisore a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa da kuma sakataren kasa bi da bi.

Kyari ya ci gaba da cewa, bisa ga kundin tsarin mulkin jam’iyyar, mataimakin sakataren jam’iyyar na kasa, Festus Fuanter, zai kasance mukaddashin sakataren jam’iyyar APC na kasa.

 

Firdausi Musa Dantsoho