Gwamnonin Gombe Da Yobe Da Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa Da Sultan Da Sauran Manyan Baki Sun Halarci Taron Rufe Gasar Karatun Alkur’an Da Aka Yi A Damaturu
Gwamnan Jihar Gombe kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya halarci bikin rufe musabaqar Alkur’ani Mai Girma ta ƙasa karo na 38 a Damaturun Jihar Yobe.
Gidauniyar Musabaqar Al-ƙur’ani a Najeriya ta Cibiyar Nazarin Harkokin Addinin Musulunci na Jami’ar Usmanu Ɗanfodio dake Sokoto, da Gwamnatin Jihar Yobe ne suka shirya gasar da nufin zaburar da matasan Musulmi wajen koyon karatun kur’ani mai tsarki da kuma haddarsa yadda ya dace; da samar da haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin musulmi da waɗanda ba musulmi ba ta hanyar ilmantar da al’ummah koyarwar Alkur’ani na gaskiya tare da aiki da shi.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu wadda ya samu wakilcin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da mai masauƙin baƙi Gwamna Mai Mala Buni, da Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar da sauran waɗanda suka yi jawabi a wajen taron sun bayyana muhimmancin Al-ƙur’ani a rayuwar Musulmi da kuma shiriyar da yake samarwa, waɗanda suka ce su ne manyan darusan da aka koya a gasar da aka kammala.
Ibrahim Mohammed Nasir daga Jihar Bauchi da Zainab Aliyu Mohammed daga Jihar Kano ne suka zama zakarun gwajin dafi na maza da mata, inda Mai Alfarma Sarkin Musulmin ya karramasu ta hanyar yi musu nadi a matsayin ‘Gwarzo’ da ‘Gwarzuwar Shekara’.
An ba su kyaututtukan motoci, da kujerun Hajji da tsabar kudi Naira miliyan 5-5 da sauran kyaututtuka.
Tawagar Jihar Gombe a gasar ba a barta a baya ba wajen nuna bajinta, inda ta samu matsayi na 7 a ɓangaren hadda da Tafsir da Qira’at daban-daban.
Gwamna Inuwa ya ziyarci rumfar Gombawa dake filin taron, inda ya tattauna da mahalarta gasar da jagororinsu, kana ya basu kyautar Naira miliyan uku.
Gwamnan na Gombe ya samu rakiyar masu girma ƴan majalisan dokokin Jihar Gombe; Hon. Siddi Buba, da Hon. Musa Buba, da Hon. Musa Manaja Zambuk, da Kwamishinonin Kudi dana bunƙasa Tattalin Arziki Muhammad Gambo Magaji, dana Kasafi da Tsare Tattalin Arziƙi Salisu Baba Alkali; dana Ruwa, Muhalli da Albarkatun Gandun Daji, Mohammed Saidu Mohammed Fawu da kuma Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jiha Sa’adu Hassan.
Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe
Hafsat Ibrahim