Ilimi Mai zurfi: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Kafa Kwamitin Da Zai Nazarci Rahotannin Kwamitocin Ziyarar Manyan Makarantun Jihar

0
41

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ya amince da kafa kwamitin da zai nazarci shawarwari da rahotannin da Kwamitocin Ziyarar Manyan Makarantun Jihar suka gabatar.

Kwamitin, wanda ya ƙunshi manyan jami’an gwamnati, zai yi cikakken nazari kan shawarwarin da kwamitocin ziyarar suka gabatar.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njoɗi wanda ya sanar da amincewar gwamnan, ya bayyana babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar a matsayin shugaba, tare da kwamishinonin ilimi, dana ilimi mai zurfi, dana kimiyya, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire, dana kuɗi da bunƙasa tattalin arziƙi a matsayin mambobi.

Haka kuma, Shuwagaban Hukumar Kula da Ma’aikata (CSC) dana Hukumar Kula da Malamai (TSC) suna daga cikin mambobin kwamitin, tare da manyan sakatarorin ofishin sake fasalin aikin gwamnati dana ayyuka na musamman, da kuma na siyasa da harkokin masarautu, wadanda za su kasance sakatarorin kwamitin.

Idan za a iya tunawa dai, kwamitocin ziyarar da Gwamnan ya kafa tun farko, sun gudanar da ayyukansu tare da miƙa cikakkun rahotanni da shawarwarinsu da nufin samar da sauye-sauye masu ma’ana don ci gaban fannin ilimi musamman a ɓangaren manyan makarantun jihar don dacewa da burin gwamnatin Inuwa Yahaya na kyautata ilimi a jihar.

Gwamna Inuwa Yahaya dai ya jajirce wajen ganin an aiwatar da sakamakon bincike da shawarwarin da kwamitocin suka bayar yadda ya dace, don samar da sauye-sauye masu tasiri da za su inganta harkokin karatu a jihar.

Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe.

 

Daga Fatima Abubakar