Kiwon Lafiya: Bagudu ya amince da zaftare kashi 3% daga albashin ma’aikatan gwamnati

0
49

Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi ya amince a cire kashi 3% na albashin ma’aikatan gwamnatin jiharsa a karkashin shirin inshoran lafiya na Kebbi State Contributory Healthcare Management Agency (KECHEMA). Wannan batu na amincewar gwamnan na zuwa ne daga bakin mai ba shi shawari kan harkokin yada labarai, Malam Yahaya Sarki a ranar Talata a birnin Kebbi, PM News ta ruwaito. Alhaji Safiyanu Garba-Bena, mukaddashin shugaban ayyuka na jihar ya ce, amincewar gwamnan ya biyo bayan bukatar da kungiyar kwadago ta gabatar a jihar. A tun farko, kungiyar ta kwadago ta nemi a cire kasho 3% daga albashin ma’aiakata tare da tura su ga asusun KECHEMA, People Gazette ta tattaro. Gwamnati ta ce: “Sanya ma’aikatan gwamnati a kan tsari a matsayin sashen doka zai baiwa hukumar damar samar da hanyoyin kiwon lafiya ga ma’aikatan gwamnati a farashi mai sauki.” A cewar gwamnatin jihar, wannan zaftare albashi zai fara aiki ne daga wannan watan na Nuwamba don turawa ma’aikatar KECHEMA ta fara shirin samar da kayayyakin kiwon lafiya ga ma’aikatan gwamnati.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho