Kofin Duniya: Benzema zai koma tawagar Faransa

0
40

Karim Benzema na iya sake komawa cikin tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya na 2022.
Tun da farko an cire dan wasan mai shekaru 34 saboda rauni.

Ana sa ran Benzema ba zai buga gasar baki daya ba saboda matsalar cinyarsa.Kociyan Faransa, Didier Deschamps, ya yanke shawarar kin kiran wanda zai maye gurbinsa, kuma ya ci gaba da daukar Kylian Mbappe, Olivier Giroud, Ousmane Dembele, Antoine Griezmann, Kingsley Coman da Marcus Thuram.

Koyaya, RMC Sport ta yi iƙirarin cewa Benzema zai iya komawa cikin tsarin Faransa yayin da ya dawo cikakken horo a wannan makon a Real Madrid.

Benzema zai iya samun saukin shiga gasar cin kofin duniya.Dokokin FIFA sun bai wa ‘yan wasan damar komawa cikin tawagarsu idan sun warke daga raunin da suka ji idan da farko an sanya sunayensu a cikin ‘yan wasan da za su buga gasar kafin a cire su.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho