Kotu ta hana ‘Yan Sanda da SSS da Kuma Sojoji Daga Korar Sarki Sanusi daga fada

0
31

Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta babbar kotun Kano da ke zamanta a kan titin Miller, ta hana ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) da sojojin Najeriya daga korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga gidan sarautar Kano.

 

Sarkin ya shigar da karar ne tare da hakimai Kano hudu: Madakin Kano Yusuf Nabahani; Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi; Sarkin Bai Mansur Adnan da Sarkin Dawaki Maituta Bello Tuta.

 

Da take bayar da wannan umarni, Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta kuma gargaɗi jami’an tsaro da kada su kama ko muzgunawa Sarkin da hakimansa.

Alkalin ta ci gaba da cewa, “An ba da umarnin na wucin gadi na hana wadanda ake amsa ake kara, ko wakilansu, daga kamawa ko gayyatar masu kara ko kuma kokarin fitar da sarkin daga gidan Rumfa har sai an saurari ƙarar da kuma yanke hukunci.

 

An bayar da umarnin na wucin gadi na hana wadanda ake kara daga yunkurin kwace tagwayen masu, hular sarautar Dabo, Takalmi mai gashin Jimina, wuka da takobin Sarkin Kano.

An kara ba da umarnin cewa wadanda ake kara Kar su sake su hana ko tsoma baki a cikin ayyukan mai kara na daya har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren karar.

 

An dage karar zuwa ranar 13 ga Yuni, 2024 don sauraren karar.