KWAMANDAN AFRICOM NA AMURKA YA ZIYARCI CDS,YA BA NAJERIYA HANYOYIN MAGANCE RASHIN TSARO.

0
8

Kwamandan rundunar sojin Amurka a Afrika, Janar Michael Langley, ya ziyarci babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, janar Christopher Musa a hedikwatar tsaro dake Abuja.

Janar Langley ya yaba da yadda Najeriya ke tunkarar matsalar rashin tsaro a kasar da kuma dabarun jagoranci a yankin. Ya kuma taya CDS murna bisa nadin da aka yi masa a matsayin Chiarman na Kwamitin Hafsoshin Tsaro na ECOWAS.

A nasa martanin CDS ya godewa kwamandan AFRICOM bisa samun lokacin da ya kawo ziyara Najeriya tare da ba da tabbacin yin hadin gwiwa da sauran kasashen yankin na kawar da duk wani nau’in ta’addanci da laifuka.

Janar Musa ya kuma nemi karin hadin gwiwar tsaro da Amurka musamman a fannin horarwa, musayar bayanan sirri da kuma saukin sayan hanyoyin da suka dace daga Amurka.

Kwamandan na AFRICOM ya samu rakiyar jakadan Amurka a Najeriya Mr Richard Mills zuwa hedikwatar tsaro.

Wannan sanarwar ya fito ne dauke da sa hannun Darakta Labarai na Helkwatar Tsaro, Brigediya Janar Tukur Gusau.

 

Daga Fatima Abubakar.