Lambar Yabo Na Jaridar The Sun: Gwamna Inuwa Ya Sake Zama Gwarzon Shekara

0
34

Lambar Yabo Na Jaridar The Sun: Gwamna Inuwa Ya Sake Zama Gwarzon Shekar

 

Makwanni biyu bayan ya lashe lambar yabo ta Gwarzon Gwamna a Fagen Ilimi, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya sake samun wani kambun daga Jaridar The Sun a matsayin Gwarzon Shekara na 2023, yayin wani biki da aka gudanar a Eko Hotel and Suites, dake Victoria Island a Jihar Legas.

Gwamna Inuwa Yahaya ya haskaka sosai yayin da ake karanto tarihinsa kafin gabatar masa da lambar yabon. An yaba masa da babbar murya game da halayensa na kwarai a matsayin jagora abin koyi.

Mataimakin Gwamnan Dr. Manassah Daniel Jatau ne ya karɓi lambar yabon bisa rakiyar Ministan Sufuri Sanata Saidu Ahmed Alkali.

Kamfanin Jaridar The Sun Publishing Limited, wacce ke wallafa jaridun Daily Sun, da Saturday Sun, da Sunday Sun da Sporting Sun, tana ɗaya daga cikin manyan jaridun Najeriya masu nagarta, wacce ta shafe fiye da shekaru ashirin a fagen yaɗa labarai.

Manajan Daraktan kamfanin, Mista Onuoha Ukey, ya bayyana cewa majalisar editocin jaridar ta baiwa Gwamna Inuwa Yahaya lambar yabo na gwarzon gwamnan na shekara ne bisa la’akari da kyakkyawan jagoranci da nasarorin da ya samu ta fuskar samar da ababen more rayuwa, da kiwon lafiya, da ilimi, da muhalli, da samar da ruwan sha, da gina jama’a da dai sauransu.

Yace sun kwatanta ayyukan na Gwamna Inuwa dana sauran takwarorinsa, inda suka gano ya yi musu fintinkau.

“Zaɓin da muka yi maka na wannan lambar yabo ya kasance ne bisa cancanta, saboda ɗimbin nasarorin daka samu a tsawon lokacin daka shafe a matsayin Gwamnan Jihar Gombe”.

Da yake miƙa lambar yabon ga Gwamna Inuwa, Shugaban taron kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya yabawa Shugaban Kungiyar Gwamnonin na Arewa bisa irin hazaƙarsa na jagoranci.

Ya kuma yabawa Gwamnan bisa yadda yake tafiyar da al’amura da yasa ya zama abin koyi, yana mai cewa jajircewa da sadaukarsa ga aiki yasa ya yi fice, ya ƙara da cewa karramawar wata shaida ce ta irin gudunmawar daya bayar da kuma jagorancinsa abun misali dake zama abin alfahari ga sauran jama’a.

 

Da yake karɓar lambar yabon ta hannun Mataimakinsa Dakta Manassah Daniel Jatau, Gwamna Inuwa Yahaya ya godewa shugabannin kamfanin na the Sun Publishing bisa yadda suka karrama ƴan nasarorin da gwamnatinsa ta cimma, inda ya bayyana karramawar da cewa ba tashi ce shi kaɗai ba har ma da tawagarsa da ɗokacin al’ummar Jihar Gombe.

Gwamnan yace “Wannar karramawa za ta ƙara zaburar da mu wajen ci gaban al’ummar Jihar Gombe, kuma za mu yi nasarar kawo sauyi don ganin Gombe ta zama jiha mai kyau da nagarta, fiye da yadda take a zuwanmu mulki.”

 

Gwamnan yace gwamnatinsa tana samar da ingantaccen shugabanci ga al’umma ta hanyar kyakkyawan tsarin ci gaban jihar na (2021 zuwa 2030) da nufin kawo sauyi a jihar nan da shekaru 10 masu zuwa, da ɗora ta kan turbar ci gaba mai ɗorewa.

 

“Mun zo da kyakkyawar manufa kuma mun tsarata yadda za ta amfane mu, muna farin ciki ganin cewa duniya tana yabawa da kyawawan nasarorin da muka samu,” in ji Gwamna Inuwa.

 

Da yake tsokaci bayan taron, Ministan Sufuri Sanata Saidu Alkali, yace yana matuƙar alfahari da irin nasarorin da Gwamna Inuwa Yahaya ya samu, yana mai cewa gwamnan ya ɗaukaka Jihar Gombe zuwa wani mataki na ƙwarai wajen gudanar da mulki da shugabanci nagari.

 

Ministan yace Gwamna Inuwa ya yi nasarar sanya Gombe ta zama abar koyi ga sauran jihohi a fagen shugabanci na gari da samar da ci gaba.

 

Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume ne ya jagoranci bikin karramawar mai cike da kayatarwa, wadda ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da Gwamnonin jihohin Ogun da Enugu, da Ministan Sufuri, Sanata Saidu Ahmed Alkali da takwaransa na Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da tattalin arziƙin zamani Bosun Tijjani, da ɗan takaran Shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023 Peter Obi, da uwar gidan Gwamnan Jihar Kwara, da Basarake Oni na Ife, da tsohon ɗan majalisan wakilai Hon Umar Ahmed Sulaiman, da shugabannin kamfanoni dana kafafen yaɗa labarai da dai sauransu.

 

Ismaila Uba Misilli

Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

 

Hafsat Ibrahim