Jerin Wadanda Suka Kafa Bankuna a Najeriya, Kamar Yadda Lawan Auwal Ya Sayi Bankin Polaris Domin Shiga jerin su Elumelu, Jim Ovia, Da Sauransu.
Babban bankin Najeriya ya bayyana cewa bangaren banki ya kunshi bankunan kasuwanci 21 Wadannan bankuna mallakin hazikan ‘yan Najeriya ne wadanda suka yi kaurin suna a fannoni daban-daban, Lawan Auwal shi ne na baya-bayan nan a jerin sunayen, bayan kamfaninsa ya kammala siyan bankin Polaris.
An bayyana Lawan Auwal a matsayin mutumin da ke bayan Strategic Capital Investment Ltd. (SCIL), kamfanin da ya sayi bankin Polaris daga babban bankin Najeriya da kuma kamfanin sarrafa kadarorin Najeriya. SCIL ta biya Naira biliyan 50 don karbe bankin kuma za ta biya karin Naira tiriliyan 1.3 nan da shekaru 25 masu zuwa. Kudaden dai CBN ne, da AMCON suka kashe wajen karbar bankin bayan an dauke su daga Skye.
Lawal Auwal, sabon mai bankin Polaris, hamshakin dan kasuwa ne kuma surukin tsohon shugaban Najeriya, Babangida ya ruwaito SCIL ta amince ta biya duk wasu makudan kudade da gwamnatin Najeriya ta kashe yayin tattaunawar.
Hukumar Harkokin Kasuwanci sun nuna cewa SCIL mallakin Ponglomerape Limited ne, wanda ke da daraktocin hukumar, Lawan Auwal, Lawan Abdullahi, Lawan Shaibu, da Lawan Jamilu. Ponglomerape Limited yana cikin kasuwancin noma , injiniyan farar hula da ci gaban ƙasa. Lawan, wanda shi ne Sarkin Sudan na Gombe , surukin Ibrahim Badamasi Babangida ne, tsohon shugaban kasar Najeriya daga 1985-1993. yana auren, Halima, Babangida a matsayin matar sa ta uku.
Daga Fatima Abubakar.