Allah Zai Zabar mana Shugaban Najeriya Na Gaba, Oba Na Benin Ya Gayawa Atiku

0
53

Oba na Benin, Oba Ewuare II, a ranar Asabar, ya shaidawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar People’s Democratic Party, Alhaji Abubakar Atiku, cewa Allah zai zabi shugaban kasar Najeriya na gaba.

 

 Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin Atiku da tawagarsa a fadar sa.

Sarkin ya yi wa Atiku fatan alheri a takarar sa na shugabancin kasar nan, ya kuma bukace shi da ya cika alkawuran yakin neman zabensa idan har ya samu shugabancin kasar.

 

 “Mai girma , muna ta bibiyar maganganunka da kuma tabbacinka, muna rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba ka lafiya da hikimar, idan ka zama zababben shugaban kasar nan.

 

 “Muna sa ka a cikin addu’o’inmu, babu shakka, za mu ci gaba da rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya zaba mana wanda zai jagoranci kasar nan. Ban ga dalilin da zai sa mu yi shakkar kowa a cikinku ba.”

 

 Tun da farko, Atiku ya bayyana Oba na Benin a matsayin daya daga cikin manyan ubannin da ke da gudunmawar da za su bayar wajen ganin an samu sauyin mulkin dimokuradiyya mai zuwa.

 

 “Kuna shugabantar daɗaɗɗen masarauta mai tarihi. Babu yadda za a yi mu zo Jihar Edo ba tare da mun kai ziyarar ban girma ba. Don haka bari in yi godiya a madadin membobin wannan tawaga da suka ba mu masu sauraro, muna kuma neman addu’o’in ku na neman sauyi a kasarmu lafiya, hadin kai, zaman lafiya da ci gaba.

Daga : Firdausi Musa Dantsoho