Lere ya Kira Ugochinyere a matsayin Hushpuppin Siyasa.

0
1

Hushpuppi na Siyasa” Ugochinyere na daya daga cikin bata-gari na PDP, yana neman kudi ne kawai ,wannan kalma dai ya fito ne a cikin wata sanarwa Mai dauke da sa hannun mataimaki na musamman Kan sadarwa na sabbin kafafen yada labarai a ofishin ministan Babban Birnin Tarayya Barr.Ezenwo Nyesom Wike

Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da sabbin kafafen yada labarai ga ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, Lere Olayinka, ya bayyana dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Ideato ta arewa da ta kudu na jihar Imo, Imo Ugochinyere Ikeagwuonu a matsayin ” hushpuppi Siyasa” wanda wani bangare na rugujewar jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ya haifar.

Olayinka, wanda ya shaida wa Ugochinyere cewa “ka daina ruruta labari kan duk wani abu da Wike ke yi,” ya gargade shi da ya fuskanci dalilin da ya sa aka zabe shi a majalisar wakilai ta yadda al’ummar mazabarsa za su daina kallonsa a matsayin wanda ya gaza.

A yayin da yake gabatar da shirin Siyasar Gidan Talabijin na Channels TV a ranar Juma’a, Ugochinyere, ya bayyana cewa Ministan Babban Birnin Tarayya da sauran Gwamnonin G5 kamar Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, da Tsohon Gwamna Samuel Ortom (Benue), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) da Okezie Ikpeazu (Abia) sun da niyyar ruguza jam’iyyar PDP.

Sai dai a wata sanarwa a Abuja ranar Asabar, Olayinka ya ce; “Wannan na daya daga cikin abubuwan da kuke samu idan aka baiwa mutanen da suka koma PDP tikitin takarar jam’iyyar ba bisa tsari ba, ya ce bata-gari a jam’iyyar PDP da ta haifar da hali irin na Ugochinyere, wanda kawai ya koma jam’iyyar a 2022 Kuma ya yi nasara.

“Saboda haka, mu a wannan bangaren ba mu damu ba saboda mun fahimci dalilin da ya sa a yanzu dole Ugochinyere ya hau kan karagar mulki ya kuma zargi Wike da taka rawar yara da kananan yara, dole ne ya gamsar da masu ciyar da shi daga Albarkatun Jihar Ribas.

Daga Fatima Abubakar.