Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Nada Farfesoshi Biyu, Dan Ajimobi, Dan Jarida, Da Wasu A Matsayin Mataimaka

0
23

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau, ya nada Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi a matsayin shugaban ma’aikata; Farfesa Bashir Muhammad Fagge, Mashawarci na Musamman (Manufa da Kulawa), da Mataimakin Babban Editan Jaridun Daily Trust, Ismail Mudashir, Mashawarci na Musamman kan kafofin watsa labarai da tallatawa.

 

A wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar ga News Point Nigeria, a ranar Lahadi, Sanata Barau ya kuma nada Idris Abiola Ajimobi, dan gidan marigayi Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan Ayyuka na musamman, Yusuf Aliyu Tumfafi, Mashawarci na Musamman kan Siyasa, Misis Ngozi Ndawi Nkemdirim, ma’aikaciyar majagaba a Majalisar Dokoki ta kasa, mai ba da shawara ta musamman kan  Gudanarwa da Shitu Madaki Kunchi, Mataimaki na Musamman kan kafofin watsa labarai da tallatawa.

Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi wanda haifaffen Faruruwa ne a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano, ya kasance shugaban Sashen Ilimi, Makarantar Cigaban Ilimi na Jami’ar Bayero Kano (BUK).

Farfesan yana da  B.A.  a Guidance and Counselling (Ed)/ Nazarin Musulunci, BUK, M.Ed/Guidance and Counseling (Unijos) da Ph.D. a Guidance and Counselling, BUK.

Bashir Muhammad Fagge, Farfesan Kimiyyar Dabbobi, dan asalin Fagge ne a karamar hukumar Fagge ta Jihar Kano. Ya halarci Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto inda ya yi digirinsa na farko a fannin Noma; da M.Sc da Ph.D a Abubakar Tafawa Balewa University.

Ya rike mukamin Provost na Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical) Bichi, Jihar Kano tsakanin 2015 zuwa 2023. Ya kasance memba a babban darasi na 40 na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Kasa (NIPSS), Kuru, Jos, Jihar Filato.

Ismail Mudashir wanda dan asalin jihar Kwara haifaffen jihar Zamfara ne. Har zuwa wannan nadin, ya kasance Mataimakin Babban Editan Jaridar Daily Trust.

A lokacin da yake Aminiya, ya rike mukamai daban-daban da suka hada da, Editan yankin (Kano), Editan Siyasa na kungiya, wakilin gidan gwamnati da kuma shugaban majalisar dokoki ta kasa. Ya fara aikin jarida ne a shekarar 2003 a New Nigerian Newspapers (NNN), Kaduna.

Ya karanta Mass Communication a Federal Polytechnic, Offa, Jihar Kwara; Kaduna Polytechnic; Bayero University Kano; da Jamia Millia Islamia University, New Delhi, India, don karatun digiri na farko da na gaba.

Firdausi Musa Dantsoho