Mutane 51 ne suka rasa rayukan su a jahar Nasarawa yayin da wani jirgin da ba san daga inda ya zo ba ya jefa musu bama-bamai daga sararin samaniya.

0
31

Wani jirgi mai saukar ungulu da ba a san ko wanene ba ya jefa musu bom din.

Yankin da ke karamar hukumar Doma yana kan iyaka da jihar Benue.

Kakakin ‘yan sandan, Ramhan Nansel, ya ce ba zai iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba.

Ya ce rundunar ‘yan sandan jihar na hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro  domin cafke wadanda suka aikata laifin.

Nansel ya ce: “Abin takaici ne cewa irin wannan abu ya faru.

Yan sanda da sauran jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana don fahimtar abin da ya kai harin tare da zakulo wadanda ke da hannu a lamarin.”

Gwamna Abdullahi Sule ya ce yana tuntubar takwaransa na Benue Samuel Ortom domin shawo kan lamarin.

Ya ce lamarin ya yi sanadiyar mutuwar makiyaya da dama, inda ya yi alkawarin tabbatar da cafke wadanda ke da hannu a kisan.

Gwamnan ya bukaci makiyayan da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa gwamnatin jihar na hada kai da Benuwai domin samun maslaha mai dorewa kan hare-haren da ake kaiwa kan iyakar Nasarawa/Benuwe.

Ya kuma kara da cewa an baza jami’an tsaro domin dakile duk wata tabarbarewar doka da oda a yankin.

Sule yace,a madadin Gwamnatin jihar na Nasarawa, yana mika sakon ta’aziyar sa ga al’ummar jihar da kuma iyalen wayanda abin ya shafa.

“Ya kara da cewa,Gwamnatin sa ba za ta yi kasa a gwiwa ba,wurin kamo wayanda suka aikata laifin tare da hukumta su.

Ciyaman na karamar hukumar Doma,Ahmed Sarki-Usman ya yaba wa jama’an yankin ganin yadda suka nutsu ba tare da ta da hankali ba.in da suka bari hukumar da ta dace ta dauki matakai.

Yayin da kuma sarkin ya musu alkawarin ganin an kawo karshen lamarin a yankin.

Shugaban kungiyar Miyetti Allah  Kautal Hore na jihar Nasarawa ,Ardo Lawal Dano,ya ce ya shiga tashin hankali kwarai da gaske,ganin irin kisan da aka yi wa mutanen sa.”Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na jihar da su shigo lamarin tare da hukumta masu hannu a  harin.

Dano ya kara da cewa,mu al’ummar ma su bin doka da oda ne,kuma ba ma son tashin hankali, don haka ya kamata Gwamnati ta yi gaggawan daukan mataki don muna cikin bakin ciki.

 

Daga Fatima Abubakar.