Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin da ta gabata a jihar Bauchi, ya bayyana cewa bai bata wa ‘yan Najeriya ba bisa alkawuran da ya dauka a yakin neman zabe a zaben 2015 da 2019.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a fadar Mai martaba Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Adamu a lokacin da ya ziyarci Bauchi a ci gaba da gudanar da gangamin yakin neman zaben shugaban kasa da na gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC)
”A lokacin da Buhari ya ga dimbin jama’ar da suka tarbe shi a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa, Buhari ya ce wannan halartar da kuka yi, ya nuna soyayya da biyayya daga yan Najeriya.
Wata sanarwa da yammacin ranar Litinin mai dauke da sa hannun mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adesina, mai taken “Na yi wa ‘yan Najeriya hidima da yabo, inji shugaba Buhari a Bauchi a lokacin da yake yakin neman zaben jam’iyyar APC. ”
Shugaban ya ce, “A kullum ina kira ga sarakuna da Gwamnoni zuwa jihohi domin nuna godiyata. kananan hukumomi, da kuma a 2019, a lokacin da nake neman tazarce a karo na biyu, na ziyarci duk jihohin tarayya da jama’ar da suka zo ganina sun fi abin da kowa zai iya saya ko talastawa, na yi alkawari cewa zan yi wa Najeriya da ‘yan Najeriya hidima gwargwadon iyawata kuma har yanzu ban bata wa kowa rai ba.”
Daga Safrat Gani