NDHS Da NPC Sun Buƙaci Haɗin Kan Jama’a Don Samun Nasarar Aikin Bincike Da Tattara Bayanan Kiwon Lafiya
Hukumar Bincike Da Tattara Bayanan Kiwon Lafiyan Jama’a ta Najeriya (NDHS) da Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) sun buƙaci haɗin kai, fahimta da goyon bayan jama’a don samun nasarar aikin tattara bayanan kiwon lafiyan jama’a na 2023/2024 dake gudana.
Da yake zantawa da manema labarai, shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa Nasir Isa Kwarra wanda Daraktan Hukumar na Jihar Gombe Jude Maigari ya wakilta, yace binciken yana da matuƙar muhimmanci wajen tsara manufofin da samar da ci gaban ƙasa.
Yace “Wannan binciken yana taka rawar gani wajen samar da bayanai masu muhimmanci waɗanda ke samar da alƙaluma kan tsara muhimman manufofi da inganta harkokin kiwon lafiya, da kuma ba da gudummawa ga muhimman ƙudurorin ci gaban al’ummarmu”.
Da yake yabawa irin goyon bayan da masu ruwa da tsaki ke bayarwa ga aikin, Maigari ya yi ƙira ga magidanta su ba da haɗin kai ga jami’an dake tattara bayanan a yankunan da aka zaba don yin aikin a faɗin jihar.
Ya kuma buƙaci sarakuna da malaman addini su wayar da kan al’amuransu kan muhimmancin wannan bincike na lafiya.
A nasa ɓangaren, Ko-odinetan Hukumar Bincike Da Tattara Bayanan Kiwon Lafiyan Jama’an ta Najeriya a Jihar Gombe Adeleke Balogun, yace binciken ba bayanai da alƙaluma kawai zai tattara ba, zai ma samar da tallafin kiwon lafiya ga jama’a don inganta lafiyar magidanta da al’ummomin da aka zaɓa don gudanar binciken a cikinsu.
Yace an zaɓi magidanta 30 a yankuna 30 a kowace jiha da Babban Birnin Tarayya, inda za a tattara bayanan yara daga haihuwa zuwa shekaru biyar, da mata masu shekaru 15-49 da kuma maza masu shekaru 15-59 a tsawon watanni shida na aikin tattara bayanan.
Hafsat Ibrahim