NDLEA ta cafke wasu mutum uku da ta jima tana nema

0
34

NDLEA ta cafke wasu mutum uku da ta jima tana nema

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta kama wasu mutum uku da ta shafe wata biyu tana farautarsu bayan da ta zarge su da ƙwarewa wajen safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu da Mozambique da ƙasashen Turai da Amurka.

Cikin wata sanarwa da hukumar ke fitarwa mako-mako, da mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya aikowa Gidan Telebijin na Tozali, ya ce hukumar ta kama mutanen ne bayan kama wata hodar ibilis mai yawa a filin jirgin sama na Legas.

Sanarwar ta ce hukumar ta samu nasarar kama biyu daga cikin mutanen da ta jima tana nema ruwa-a-jallo, wato Onyinyechi Irene Igbokwuputa da kuma Frankline Uzochukwu ranar Juma’a 19 ga watan Afrilu a filayen jirgin saman Legas da na Awka.

 

Sai kuma Osita Emmanuel Obinna wanda ta kama shi a birnin Legas.

 

 

hukumar ta kuma ce takama wani mutum da ya yi yunƙurin fita da tabar wiwi da nauyinta ya kai kilogiram 9.80, daga Najeriya zuwa ƙasar Oman.

‘Bayan hukumar ta kama shi ya bayyana cewa an ƙulla yarjejeniyar cewa za a biya shi naira miliyan 1,200,000 idan har ya fitar da tabar zuwa Oman.

Babafemin ya kuma ce a ranar 20 ga watan Afrilu hukumarsa ta kama wani direban mota a Girei kan hanyarsa ta zuwa Mubi, inda jami’an hukumar suka kama ƙwayar ‘opioids’ da ke sa maye da yawanta ya kai miliyan 1,250,000 mai nuyin kilogiram 450.

 

Shamsiyya Hamza Sulaiman