Ministan Labarai ya yabawa wakilan Najeriya na taron fasahar kere-kere ta duniya.

0
17

Ministan Labarai ya yabawa wakilan Najeriya na taron fasahar kere-kere ta duniya

 

Daga: Muhammad Suleiman Yobe

 

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ya yabawa tawagar da zata wakilci Najeriya

a taron fasahar kere-kere ta duniya da za ayi a birnin Dallas na jihar Texas ta Amirka a karshen wannan watan.

 

Mataimakin Darakta, Ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta kasa Suleiman Haruna ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ciki harda gidan Telebijin na Tozali.

 

Inda ya ce ministan ya yabawa tawagar ne a lokacin da suka kai masa ziyarar ban girma a ranar Juma’a, 19 ga Afrilu, 2024.

 

Ministan ya yi farin cikin karbar tawagar wanda suka ƙunshi ɗaliban masu shekaru 15 zuwa kasa na makarantar Glisten, Abuja, waɗanda suka samu rakiyar masu horar da su.

Mohammad ya ce gwamnati tarayya na son ‘yan Najeriya su na samun ɗaukaka hakan ne yasa suke tallata ’yan Nigeriya domin anan gaba ƙasar tayi alfahari da su.

Ministan ya ce ya samu kwarin gwiwa bisa basirar da yaran suka nuna a gabansa, ya kuma ji dadin abubuwan da suka kirkira.

Ya ce kokarin wadannan yaran abun koyi ne ga ƴan Nijeriya domin yana nuni da cewa idan aka basu dama, zasu yi fice sannan Nijeriya zata yi alfahari da su.

Ya yi alkawarin tallafa wa tawagar wajen basu walwala a lokacin da suke gudanar da gasar.

 

Tun da farko, shugaban tawagar, Abubakar Mohammed, ya yabawa Ministan bisa kyakkyawan aikin da yake yi na ciyar da Najeriya gaba, ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su san cewa ana wakiltarsu a wannan gasar.

Ya ƙara da cewa jajircewar yaran na nuni da cewa makomar kasar za ta yi kyau anan gaba.

Anashi Babban Darakta na makarantar Glisten, Abba Said, ya ce gasar ta ƙunshi kungiyoyi 650 daga kasashe 65.

Ya ƙara da cewa, duk da cewa ba wannan ne karon farko da Najeriya ke halarta gasar ba, amma a wannan karon tabbas zasu dawo gida da kyaututtukan saboda fadada gasar da aka yi da wasu gasanin na’urori na zamani.

Kawo yanzu dai Yara 11 ke wakiltar Najeriya kuma zasu fafatawa ne a rukunai uku na gasar.

 

 

 

Hafsat Ibrahim