Kungiyar Qismud-da’awa karkashin jagorancin Malama Halimatu Saeed ta rufe taron tafsir na watan Ramadan rana ta 23 sherkara 1443 da ya zo daidai da 24 ga watan afrilun 2022 da take kaddamarwa daga littafin Alqurani mai girma tare da mai ja mata baki Malama Hauwa’u Muhammad cikin suratul Nur.
Suratul Nur ita ce surah ta 24 a Alqur’ani mai girma kuma tana da ayoyi 64,surar tana magana akan al’amura da ta shafi al’umma kamar Zina,hukunce-hukunce na sharia,ladubba, falala da Rahamomin Ubangiji ga bayinsa , tarbiya da sauran su.
Malama Halima, ta yi Jan kunne da gargadi ga jama’a baki daya da mu kiyaye dokokin Allah, mu kauce wa aikata fasadi a bayan kasa,mu kiyaye aikata haraam tare da rungumar Halas da bautawa Allah kamar yadda ya shar’anta a Alqurani mai girma da Hadisan Annabi Muhammad (SAW).
Malama ta kara da cewa bin Allah da manzon Sa kamar yadda sharia ta tanada shi zai kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya.Ta roki Allah da ya shiryar da mu kan hanya madaidaiciya,Ya mana afuwa kan kurakuren mu ya kuma ba mu ikon aikata alkhairi.
Ta kara da cewa,acikin wannan wata mai albarka,mu dage da ibada,adduo’i ,hailala,istigifari domin ceto kasar mu daga halin ta ke ciki.Ta ce musamman a goman karshe mu yawaita cewa ÀLLAHUMMA INNAKA AFUWUN TUHIBBUL AFUWA FA AFU’ANNA,da kuma taubatan nasuha wato tuba dawwamamiya,domin Allah SWT Ya Yi alkawarin yafe wa bawan sa in har idan ya tuba kuma ya daina.
Daga Fatima Abubakar
,